Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon shugaban ?asa Goodluck Jonathan ya garga?i ?an Najeriya da kada su kuskura su za?i masu kashe mutane a za?e mai tafe.
Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a garin Uyo na Jihar Akwa Ibom a taron addu’o’i da aka yi kan cikar jihar ta Akwa Ibom shekara 35 da samun jiha.
“A shekarar 2023, kada ku yi kuskuren za?en masu kashe mutane,” in ji Jonathan. Wa?anda za su ?auki wu?a?e da bindigogi da duk sauran makamai su je su kashe mutane saboda siyasa ma?iyan al’umma ne. Idan ka kashe wani domin ka zama shugaba, za ka ci gaba da kashewa domin ka kasance shugaba,” kamar yadda Mista Jonathan ya bayyana.
Haka kuma Mista Jonathan ?in ya yaba wa Gwamnan Udom Emmanuel na jihar kan ayyukan ci gaba da ya kai jihar.
