Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan al?awurran da Gwamnatin Tarayya ta sha yi wa ?ungiyar Malaman Jami’o’i ta ?asa (ASUU), cewa za ta biya bu?atun su domin su daina yajin aiki, a yau kuma gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da ku?a?en da za ta iya biya wa malaman jami’o’i bu?atun da suke nema ?in.
Ministan ?wadago Chris Ngige ne ya bayyana haka yayin da Gidan Talabijin na Channels ke hira da shi a ranar Alhamis.
Kafin tafiyar ASUU yajin aiki makonni biyu da suka gabata, ?ungiyar ta ce duk da alwashi da al?awarin da gwamnatin tarayya ta ?auka bayan masu shiga tsakani, har da shugabannin ?angarorin addinai sun sa baki, har yau gwamnatin ba ta cika alkawari ko ?aya ba.
Idan ba a manta ba kuma, bayan an shiga tsakani a cikin watan Janairu, ASUU ta ce “idan malaman jami’o’i su ka sake tafiya yajin aiki, to a tuhumi Buhari, shi ne bai cika al?awari ba.
Babba daga cikin al?awarin da har yau aka kasa cika wa ASUU shi ne wanda Gwamnatin Tarayya ta ?auka a rubuce (MOU) cewa za ta aiwatar (MOA), kuma ta sa hannu tun a cikin 2009.
