Daga Adamu Shehu Bauchi
Munsan ba muyi ma Mutanen karamar hukumar Toro aiki ba tun lokacin da muka hau karagar mulki har zuwa yanzu saboda haka ina ba mutanen toro hakuri ba wai mun manta da ku bane sai don karancin kudade a hannun Gwamnatin Jihar Bauchi.
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ne yayi wan nan kalami a ranar Azabar, lokacin da yakai kayan tallafi ma al’ummar karamar hukumar Toro a babban filin wasa na karamar hukumar.
Gwamnan yace zamu bude ayyukan more rayuwa cikin kankanin lokacin da yage ma gwamnatin mu a karagar mulki, Kamar hanyoyi masu muhimanci ga daukacin al’umman yankin Toro, Kamar hanyar Rishi zuwa Tulu da hanyar Gumau da sauransu.
Saidai Gwamnan yace sunyi abubuwa da yawa ta bangaren makarantu don samar da Ilimi mai inganci ga dumbin matasan yankin toro, da bangaren kiwon lafiya
A wajen taron bada kayan tallafin, Bala ya kara da cewa”Mun kawo kayan tallafi na kimanin miliyan bakwai 7 zuwa miliyan takwas 8 don rage radadin talauchi da ake fama dashi a ko’ina a halin yanzu a kasa baki daya
Kwamishinan Ilimi na Jihar kuwa a wajen taron Dokta Aliyu Tilde ya yabawa Gwamnan da ya kawo kayan tallafi ma masu karamin karfi a Karamar hukumar Toro, don suci gaba da kananan sana’oinsu domin dogaro da kai, a cikin wani shiri na musamman da Gwamnan ya shirya na yaki da talauchi a fadin jihar
Mutane dari biyar ne zasu cibgajiyar wan nan Kayayyakin tallafin da aka raba a wajen taron, wadanda suka hada da Injin Markade, Keken Dinki, Motoci Kirar Sharon, Mashina Kirar Bajaj, Akuyoyi da Kuma tsabar kudi naira dubu Hamsin ga masu kana nan Sana’o’i a yankin Toro.
Wadan da suka samu tallafin su kimanin mutane dari biyar tsakanin Mata da matasa da dattijai duk a yankin, karamar hukumar, kana sunyi godiya da kuma fatan alheri ma gwamnatin jihar baki daya.
