Ba Mu Sanar Da Ranakun Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara Ba – Gwamnatin Tarayya

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta karyata wani labari da a ke ya?a wa a kafafen ya?a labarai da ake ala?anta shi da ma’aikatar cewa ta bayar da sanarwar hutun bukukuwan Kirsimeti.

Kakakin ma’aikatar, Afonja Ajibola, a ranar Asabar a Abuja, ya ce ma’aikatar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan hutun bukukuwan Kirsimeti.

Kakakin ya ce labarin da kafafen yada labarai ke yadawa karya ne, domin har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta ayyana ranakun hutu a hukumance ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na ?asa ya bayar da rahoton cewa, wasu kafafen yada labarai a ranar Juma’a, sun bayar da rahoton cewa gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun 26, 27 ga watan Disamba da 2 ga watan Janairu, 2023, a matsayin ranakun hutu.

Ma’aikatar ta shawarci jama’a da su yi watsi da labaran da ke faruwa, su kuma jira sanarwar da jama’a za su fitar kan lamarin nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

Related posts

Leave a Comment