Maaikatar harkokin cikin gida ta karyata wani labari da a ke ya?a wa a kafafen ya?a labarai da ake ala?anta shi da maaikatar cewa ta bayar da sanarwar hutun bukukuwan Kirsimeti.
Kakakin maaikatar, Afonja Ajibola, a ranar Asabar a Abuja, ya ce maaikatar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan hutun bukukuwan Kirsimeti.
Kakakin ya ce labarin da kafafen yada labarai ke yadawa karya ne, domin har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta ayyana ranakun hutu a hukumance ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na ?asa ya bayar da rahoton cewa, wasu kafafen yada labarai a ranar Jumaa, sun bayar da rahoton cewa gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun 26, 27 ga watan Disamba da 2 ga watan Janairu, 2023, a matsayin ranakun hutu.
Maaikatar ta shawarci jamaa da su yi watsi da labaran da ke faruwa, su kuma jira sanarwar da jamaa za su fitar kan lamarin nan da yan kwanaki masu zuwa.

