Shugaban Hukumar Za?e ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu ya jaddada shirinsu na gudanar da babban za?e na 2023 a lokacin da aka tsara, yana mai cewa “ba mu ta?a tunanin ?age za?en ba”.
INEC ta tsara gudanar da za?en daga ranar 25 ga watan Fabarairu mai zuwa, inda za a za?i shugaban ?asa da ‘yan majalisar tarayya, daga baya kuma a za?i gwamnoni da ‘yan majalisar jiha a watan Maris.
Sai dai yayin wani taro a farkon makon nan, wani babban jami’in Inec ya bayyana cewa idan ba a ?auki matakan da suka dace ba matsalolin tsaro za su sa a ?aga za?en a wasu yankunan Najeriya.
“Inec ba ta da wani tunanin sauya jadawalin za?en ballantana ma ?age shi. Irin tabbacin da jami’an tsaro suka ba mu na tsaron lafiyar ma’aikatanmu ya ?arfafa mana gwiwar ci gaba da shirye-shiryenmu,” in ji farfesan a ranar Laraba.
Ya ba da tabbacin ne yayin da ya gana da jam’iyyun siyasa 18 da za su fafata a za?en, inda ya gabatar musu da kundin rajistar masu ka?a ?uri’a da yawansu ya kai miliyan 93.4.
“Babban za?en 2023 zai gudana yadda muka tsara shi. Duk wani rahoton da ya ruwaito sa?anin haka ba matsayarmu ba ce,” kamar yadda ya jaddada.
