A yayin da rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna ta fara bincike a daren yau kan rasuwar da ake cewa jarumar Kannywood Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta yi, wani mutum wanda ba a san ko waye ba ya fa?a wa iyalin ta cewa gobe za su kai gawar ta gidan su a Kano.
A daren yau ne dai labari ya ?ulla cewa fitacciyar jarumar ta mutu a gidan wata ?awar ta mai suna Khairat a Kaduna.
An ga sa?o an wallafa a shafin Zee-Zee na Instagram da sunan jarumar wai ta rasu a Unguwar Sarki.
Sa?on ya ba mutane mamaki, musamman da yake daga shafin jarumar aka tura shi, wanda hakan na nuni da cewa duk wanda ya tura sa?on, to wayar Zee-Zee na hannun sa.
Binciken da mujallar Fim ta yi a daren nan ya gano cewa wani wanda ke i?irarin sunan sa Sufeto Khalid ya fa?a wa iyalan jarumar cewa wai ya kama Khairat da mijin ta, kuma ya na tsare da su a wani ofishin ‘yan sanda a Kaduna.
Mutumin ya tabbatar wa da iyalan jarumar cewa Zee-Zee ta rasu, wai za su kai gawar ta Kano a gobe.
Sai dai Khalid ya ?i fa?in a wane ofishin ‘yan sanda ake tsare da wa?anda aka kama, sannan ya ?i bada lambar wayar sa ko lambar Khairat ?in.
Ta wayar Zee-Zee ake magana da shi lokacin da aka kira wayar tata.
Khalid ya bar ?anwar Zee-Zee, wato Hadina ?an-Chaina, da sauran dangin ta cikin zullumi da damuwa, ran su cike da tambayoyi.
Sun zura wa sarautar Allah ido har zuwa gobe su ga me zai biyo baya.
Da mujallar Fim ta tuntu?i kakakin rubdunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna game da i?irarin da Khalid ya yi, sai ya ce su kam wannan nagana ba ta iso gare su ba.
Kakakin, ASP Muhammad Jalige, ya ce akwai tababa kan maganar da mutumin ya yi domin ba haka ‘yan sandan gaske ke yin aikin su ba.
Ya ce in da gaskiya ne, to da nan da nan za a sanar da hedikwata domin “ba a Division ake ‘handling case’ da ya shafi kisa ko mutuwa ba.”
Duk da haka, ya bada tabbacin cewa rundunar ‘yan sandan za ta binciki al’amarin domin gano bakin zaren, kuma duk abin da ta gano za ta sanar ba tare da ?ata lokaci ba.
A wani ?angaren kuma, mujallar Fim ta tuntu?i wata hukumar tsaro a Kaduna don jin abin da hukumar ta sani game da wannan al’amari.
Hukumar ta kar?i lambar wayar Zee-Zee a wajen wakilin mu, ta ce za ta bincika ta gani idan jarumar na cikin Jihar Kaduna.
Bayan wani ?an lokaci sai hukumar ta sanar da wakilin mu cewar binciken su ya nuna masu cewar wayar Zee-Zee ba ta cikin Jihar Kaduna, ta na can cikin Sabon Garin Kano.
“Ba mu ce mai wayar na da rai ko ba ta da rai ba, amma dai wayar ta ba ta cikin Jihar Kaduna,” inji hukumar.
MAJIYA: Fim Magazine
