Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitaccen malamin addinin musulunci, Dr Sheikh Ahmad Gumi ya ?aryata cewa hukumar tsaron farar hula, DSS, ta gayyace shi, domin amsa wasu tambayoyi akan kalaman da ya yi a Arise TV.
Ba sabon abu bane hukumar ta gayyaci duk wani da ta ke son yi wa tambayoyi,” inji shi Amma a wata hira ta musamman da ya yi da manema labarai a gidanshi dake Kaduna, Gumi ya ce babu wanda ya gayyace shi.
Dr Gumi ya bayyana cewar wasu da suka ?osa su ga an kama shi ne suka ?ir?iri labarin.
Malamin addinin musuluncin ya ce duk lokacin da ya ke son shiga daji domin ya tattauna da yan bindiga, ya kan tuntubi jami’an tsaro, hakimai da wasu jami’an gwamnati kafin ya tafi.
“Babu wanda ya gayyace ni. Kafafen watsa labarai ne ke son kawo rudani kuma da izinin Allah ba za su yi nasara ba. Muna tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaro amma ba a gayyace ni ba,” in ji shi.
Da aka masa tambaya ko ya ga rahoton cewa DSS ta gayyace shi, ya ce: “Eh, na karanta amma dariya kawai na yi. Na ce bari in kyalle su suyi farin ciki kan abin da suke tunanin rugujewa na ne amma karya ne, ba a gayyace ni ba.”
VOA Hausa ta ruwaito cewa mai magana da yawun Gumi, Tukur Mamu, yana cewa an gayyaci Sheikh din zuwa ofishin DSS a Kaduna.
