Tsohon kakakin majalisar wakilai ta Najeriya Ghali Umar Na’Abba ya zargi gwamnoni da cewa su ne matsalar Najeriya da ke kassara dimokaradiyya a ?asar.
A hirarsa da BBC ya ce gwamnoni suka haddasa duk wani halin da yanzu Najeriya ta tsinci kanta a ciki.
Duk ana ganin dimokaradiyya a Najeriya wuyanta ya isa yanka, amma tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriya na ganin da sauran aiki idan aka yi laakari da manyan matsalolin da suka dabaibaye dimokuradiyyar Najeriya, a cewarsa saboda rashin dimokaradiyyar cikin jamiyya da siyasar uban gida da kuma siyasar ?angaranci.
NaAbba wanda aka za?a ?an majalisar tarayya a jamiyyar PDP kafin ya koma APC, ya ce yanzu dukkanin manyan jamiyyun babu wadda take bin tsarin dimokuradiyya.
Yanzu ba ni da jamiyya saboda ba dimokuradiyya ake ba, kuma ba a yin za?e.
Na janye daga takarar sanata saboda an bukaci dole sai na bayar da kudi a tsayar da ni, in ji shi.
Ya shaida wa BBC cewa suna shirin kafa sabuwar jamiyyarsu kuma zai nemi takarar kujerar sanata.

