Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta ce karin da aka samu a farashin wasu kayan abinci, fetur, diesel da sauran kayayyaki abune da ake fama da shi a duniya gabaki daya, ba wai iya wata kasa bace.
Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya kara da cewar gabatar da lamarin a matsayin matsalar Najeriya makirci ne, rashin gaskiya da kuma batarwa na ‘yan adawa.
“Wannan kididdiga da ake amfani da shi makirci ne karara. Wadanda ke yayata wannan alkaluman ba tare da daura su a ma’auni ba rainin wayo ne da su. “Mu duba farashin kayan abinci da fetur. Ku duba farashin kayan abinci a sauran kasashe, musamman Ingila da Amurka.
Ministan ya kara da cewar karancin man fetur da aka samu a fadin kasar a kwanan nan ya fara yin sauki, yayin da matakan da gwamnati ta dauka ya fara aiki. Ya jadadda cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu gagarumin nasarori a dukkan bangarori, duk da matsalolin da kasar ke fuskanta.
“Yan Najeriya na cikin dimuwar mulkin zaluncin PDP na shekaru 16, kuma ba za su koma ruwa ba ta hanyar barinsu su koma kujerar mulki ba.”
