Asiri Ya Tonu: An Gano ?ungiyar Kasar Faransa Dake Koya Ta’addanci A Borno

Rahotanni daga Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin dakatar da ACTED, wata ?ungiyar agaji ta Faransa mai zaman kanta da ake zargin tana bayar da horon harbin bindiga a wani otal a Maiduguri.

Sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar ranar Asabar ta ce ?ungiyar na gudanar da atisayen koya wa mutane harbi.

Gwamnatin Borno ta ce mutanen unguwar da ke kusa da otal ?in ne suka bayar da rahoton cewa suna jin ?arar harbin bindiga.

“Kuma bayan sanar da rundunar ?an sanda da suka gano ginin otal ?in, an samu ?ananan bindigogi na koyon harbi guda uku, mutum biyu da ake ba horo, dukkaninsu ?an Najeriya suna hannun ?an sanda ana bincike,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ?ara da cewa yayin da ?an sanda suka ?addamar da bincike, Gwamna Zulum ya bayar da umarnin rufe otal din tare da dakatar da ACTED daga duk wani aikin jin ?ai a jiharsa ta Borno

Related posts

Leave a Comment