Tsohon Shugaban ?asa, Olusegun Obasanjo ya maida wa dattijon Neja-Delta Edwin Clark kakkausan raddin cewa arzikin fetur ?in da ?asar nan ke da shi, na Najeriya ne, ba na Neja-Delta ba.
Cikin wasi?ar da Obasanjo ya aika wa Clark a ranar Talata, kuma ya raba wa manema labarai a Abeakuta, Obasanjo ya ce ?arya Edwin Clark ke yi da ya ce wai shi Obasanjo ?in ba ya ?aunar yankin Neja-Delta.
“Kowa ya san ni a ?asar nan, na da?e ina kishin zamantakewar Najeriya a matsayin ?asa ?aya dun?ulalliyar. Babu ruwa na da fifita shiyya ko yanki.”
Kamfanin Dillacin Labarai ya ruwaito Edwin Clark na cewa Obasanjo ya na jin haushin yankin Neja-Delta.
Clark ya yi furucin a wurin ne a wurin taron ?abba?a zaman lafiya, wanda Global Peace Foundation and Vision Africa ta shirya, kwanan nan a Abuja.
Zarge-zargen da Clark ya yi wa Obasanjo na cikin wata wasi?ar da ya aika wa tsohon shugaban na Najeriya.
A cikin raddin da Obasanjo ya yi wa Clark, ya ce masa ba daidai ba ne, Clark ko wani ?an Neja Delta ya ri?a cewa arzikin man fetur ?in ?asar nan na yankin Neja Delta ne.
A kan haka Obasanjo ya ce mai Najeriya ce ke da duk wani albarkatun ?ar?ashin ?asa, ba yankin da albarkatun ?asar su ke ne ke da ha??in sa ba.
A cikin wasi?ar wadda Obasanjo ya yi wa dattijo Clark kaca-kaca, ya kira shi mai magana ya na sakin-baki, kuma bagidajen da bai waje da duniya ba.”
Obasanjo ya ce bai kamata dattijo kamar Clark ya na zantuka irin na mashaya ba.
