APC Ta Sanar Da Ranar Gudanar Da Babban Taro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana ranar da za’a gudanar da tarukan jam’iyya a matakin jihohi 36 na Najeriya har da Abuja.

Kwamitin ya sanar da cewa za’a gudanar da gangamin tarukan APC a matakin jihohi ranar Asabar, 2 ga watan Oktoba, inda za’a zabi shugabannin APC a jihohi.

Wannan na kunshe ne a wani gajeren jawabi da sakataren kwamitin rikon kwarya na APC ta kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Bugu da kari, sakataren ya sanar da cewa jam’iyyar zata fara siyar da fom na gangamin tarukan daga ranar Laraba, 15 ga watan Satumba, na wannan shekara da muke ciki ta 2021.

Jam’iyyar APC ta fara gudanar da tarukanta ne daga matakin gundumomi, inda aka gudanar da za?en shugabannin APC a matakai daban daban. Tarukan APC na gundumomi ya gudana ne ranar 31 ga watan Yuli 2021, yayin da na kananan hukumomi ya gudana ranar 4 ga watan Satumba.

Related posts

Leave a Comment