Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta bayyana babban dalilin da yasa ta dakatar da ayyukan kamfanonin sadarwa a jihar Zamfara, a daidai lokacin da jami’an tsaro suka tsaurara kai hare hare yankin.
Gwamnatin tace ta katse hanyoyin sadarwa a jihar bisa yawaitar ayyukan yan Bindiga ne saboda hukumomin tsaro sun bu?aci hakan, kuma cikin gaggawa gwamnati ta amince da hakan.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Dakta Isa Pantami, shine ya bayyana haka ga manema labarai jim ka?an bayan fitowa daga taron majalisar zartarwa (FEC) ranar Laraba a Abuja.
Ba hakanan muka ?auki matakin ba, shawarar jami’an tsaro muka bi, Pantami yace ba ma’aikatarsa ce ta kirkiri katse layukan sadarwa ta hanyar dakatar da ayyukan kamfanonin sadarwa a jihar ba.
Sheikh Pantami ya ?ara da cewa lokacin da hukumomin tsaro suka gabatar da bukatarsu a matsayin hanyar dakile ayyukan yan bindiga, gwamnatin tarayya ba ta musa musu ba.
“Ba wai hakanan muka ?auki wannan matakin ba, hukumomin tsaro ne suka bukaci hakan domin zai taimaka wurin dakile ayyukan yan bindiga.” “Lokacin da suka gabatar da bukatar haka bamu da wani za?i, gwamnati a shirye take ta hakura da abinda take samu a ?angaren domin samun zaman lafiya”
Malam Pantami ya bayyana cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta sadaukar da duk abinda take samu daga ?angaren kamfanonin sadarwa domin samun tsaro a ?asa.
Ministan ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su fahimci matakan da aka ?auka kuma su bada goyon bayan su ga jami’an tsaro wajen kawo ?arshen lamarin.
