An Zo Wajen: El Rufa’i Ya Cire ‘Danshi Daga Makarantar Gwamnati

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana dalilin da ya sa ya cire ?ansa a asirce daga makarantar gwamnati da ya saka shi.

Jaridar Daily Trust ce ta fara ruwaito yadda gwamnan ya cire ?an nasa mai shekara shida daga makarantar Kaduna Capital wanda ya saka shi a 2019.

Cikin wata hira da BBC Pidgin, El-Rufai ya ce ya cire shi ne saboda yadda ‘yan fashin daji ke ?o?arin kai wa makarantar hari domin sace yaron nasa, musamman saboda a kare rayuwar sauran yara.

Ya ?ara da cewa ya saka ‘yarsa ma mai suna Nesrin a makarantar lokacin da ta cika shekara shida da haihuwa.

“Mun cire su ne na ?an wani lokaci saboda tsaron makarantar, saboda mun da?ile harin ‘yan fashi har sau biyu a kan makarantar da ke yun?urin sace ?ana.

“Ba na tunanin za su samu nasara saboda akwai cikakkun jami’an tsaro a wurin amma za a saka rayuwar sauran yaran cikin ha?ari…suna so su ga idan suka sace ?an nawa zan biya ku?in fansa ko ba zan biya ba.”

Gwamnan ya ce yanzu haka yaran suna gida, inda ake yi musu darasi amma za su rubuta jarrabawa a makarantar.

Related posts

Leave a Comment