Kungiyar ‘Yan Kishin Kasa Sun Bukaci Tinubu Ya Kori Shugabar NIPOST

images 2024 03 30T164819.671

Wata Kungiyar Masu Kishin kasa ta bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya Sauke Shugaban hukumar aikawa da sakonni ta kasa NIPOST Tola Odeyemi, Saboda rashin sanin makamar aiki.

Masu kishin kasan Sun bayyana hakan ne a Cikin wata Sanarwa da suka fitar a Abuja, Karkashin Jagorancin Kwamared AbdulWahab Tajuddeen, inda suka zargi Tola Odeyemi da karya ka’idojin aikin gwamnati.

Acewar Masu korafin Shugaba hukumar tana barin kayayyakin jama’a na lalacewa a ofisoshin hukumar musamman a jihar Legas da kuma Abuja.

Haka kuma, suna Zarginta da rashin zama a ofishinta inda acewarsu takan shafe fiye da mako guda bata je ofis ba.

Kazalika, sun kuma koka kan yadda Tola Odeyemi ta aje Wasu Mata da ba ma’aikatan hukumar ba a ofishinta wanda hakan Acewar su ya saba dokar aiki.

Akan hakan tawagar ‘yan kishin kasar, karkashin jagorancin Kwamared AbdulWahab Tajuddeen sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki mataki akan shugabar ta Nipost.

Sai dai duk kokarin da aka yi na jin Ta bakin Shugabar ko mai magana da yawunta akan wannan zargin ya ci tura.

Related posts

Leave a Comment