An Yanke Wa Indiyawan Da Suka Kashe Wani Musulmi Daurin Shekaru Goma

Wata kotu a Indiya ta yanke wa wasu maza 10 hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari saboda samun su da laifin dukan wani musulmi har ya mutu, shekaru hudu da suka gabata.

Tabrez Ansari, mai shekaru 24 ya mutu ne kwanaki ka?an bayan harin da wasu mutane suka kai masa bayan sun zarge shi da satar babur a jihar Jharkhand da ke gabashin ?asar.

Wani faifan bidiyo da aka ri?a ya?awa, ya nuna yadda aka tilasta wa marigayin ya yi kalaman yabo ga abin bauta na addinin Hindu, yayin da yake magiya tare da ro?on kada a kashe shi.

Lamarin ya haifar da cece-ku-ce tsakanin al’umma.

Iyalin matashin sun zargi ?an sanda da hana su ganin ?an nasu.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta musanta hakan.

Bidiyon da aka ri?a ya?awa da aka ?auka a daren 19 ga watan Yunin 2019 ya nuna Ansari cikin halin ban tausayi, kuma daure a jikin sandar wutan lantarki cikin taron mutane, yayin da jini da hawaye ke gudana a fuskarsa

Related posts

Leave a Comment