An Kama Gawurtattun ‘Yan Luwadi Biyar A Katsina

Kimanin Mutum 5 ne da Suka yi lalata da ?an shekaru 17 suka fa?a tarkon hukuma, wasu mutane su 5 sun shiga hannun jami’an Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina

Kakakin Rundunar SP Gambo Isah ne ya gabatar da wa?anda ake zargin ga ?an jaridu a lokacin wani taron manema labarai da ya gudana a Farfajiyar Hedikwatar ?ansandan ta jihar Katsina.

Wa?anda ake zargin dai sun aikata lalata da yaron a lokuta daban-daban, kuma a wurare maban-banta. Kamar yadda SP Gambo Isah ya bayyana sun ha?a da; Ibrahim Amadu, ?an kimanin Shekaru Arba’in da Biyu 42 dake Sabuwar Unguwa Quarters, Katsina, Saminu Abdullahi, ?an Shekaru Ashirin da Biyar 25 daga Unguwar Farin Yaro Katsina.

Sauran sun ha?a da Jamilu Ibrahim, ?an kimanin Shekaru Hamsin 50yrs shima daga Farin Yaro Quarter, Katsina, Bashir Lawal, mai Shekaru 30yrs dake Gangaren Tudun Yanlihida Quarters, Katsina, da kuma Mohammed Sani, ?an Shekaru 30yrs of Salauwa Quarters, Katsina.

Yaron da akayi lalatar dashi ya bayyycewa wani Ibrahim Amadu ?aya “daga cikin wa?anda ake zargin yayi barazanar yanka shi da wu?a a dai-dai lokacinda ya bukaci yin lalata da shi” yayinda ya ?aure mashi hannuwa yayi lalata dashi, kazalika ya bayyana cewa sauran wadanda make zargin ma sunyi mashi haka, akwai ma wasu Mutane Shidda da yanzu haka ake nema ruwa a jallo.

A lokacin gabatar da wa?anda ake zargin, manema labarai sun zanta da su kuma dukkansu sun amsa laifin aikata lalata da yaron a lokuta daban-daban.

Daga bisani, Kakakin Rundunar ‘Yan sandan ya tabbatar da cewa “za a gurfanar da su a gaban ?uliya da zaran an kammala bincike, domin girbar abinda suka aikata”.

Related posts

Leave a Comment