Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al’umma, musamman matasan ?asar da su ?ara ha?uri kan halin matsin rayuwa da suke fuskanta a yanzu.
Tinubu ya bayar da tabbacin cewa wahalhalun da ?an Najeriya ke fuskanta a yanzu za su zamo da?i a nan gaba.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a fadar gwamnatin ?asar yayin da ya kar?i ba?uncin shugabannin matasa na jam’iyar APC daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ya shaida wa matasan cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da matasa a dukkan matakan da za ta ri?a ?auka, ya kuma ?ara da cewa “ba zai yi shakkun ?aukar kowane mataki da zai kawo ci gaba da ha?in kan ?asa ba.”
Shugaba Tinubu ya ce ya fahimci irin ra?a?in da ?an ?asar ke ciki “Na yi rantsuwa ga ?asata cewa ba zan yi shakkar ?aukar kowane irin matakin da zai samar da ci gaba da tabbatar da ha?in kan ?asar nan ba.
“Matakan farfa?o da tattalin arziki kan ?auki lokaci kafin a fara ganin alfanunsu. Ku ?ara ha?uri ka?an.
