2023: Dole Shugabancin Kasa Ya Koma Kudu – Gwamnonin Kudu

?ungiyar gwamnonin jihohin kudancin Najeriya ta ce dole shugabancin Najeriya ya kasance na kar?a-kar?a daga yankin arewaci zuwa kudanci, kuma tana son shugaban ?asa da za a za?a nan gaba ya fito daga yankin kudancin Najeriya.

Kungiyar ta tsayar da wannan matsaya ne bayan kammala taron gwamnonin kudancin ?asar a ranar Litinin a Lagos.

Gwamnonin kuma sun amince da wasu bu?atu da suke son a aiwatar da suka shafi tsaro da yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima da kuma dokar man fetur.

A sanarwar da gwamnonin jihohin kudancin ?asar suka fitar ta jaddada bu?atar tabbatar da mulki ya dawo kudancin ?asar kan abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci tare da sake jaddada goyon baya ga ha?in kan Najeriya.

Taron na zuwa bayan samamen da hukumomin tsaron Najeriya suka kai gidan jagoran fafutikar i?irarin kafa ?asar ?abilar yankin Yarbawa inda aka samu makamai a gidansa.

Sauran bukatun na ?ungiyar gwamnonin kudancin Najeriya sun ha?a da:

  • Tabbatar da bukatar ?an sandan jiha
  • Dole wata hukumar tsaro ta nemi izininsu kafin ?addamar da samame a jihohinsu
  • Sun tsayar da ranar 1 ga Satumban 2021 da dokar hana kiwo za ta fara aiki a dukkanin jihohin kudanci
  • Kungiyar kuma ta za?i Lagos a matsayin hedikwatar ?ungiyar gwamnonin kudancin Najeriya

Related posts

Leave a Comment