Rahotannin dake shigo mana yanzu na bayyana cewar Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kame wasu malamai da jami’an da ke kula da shirin ciyar da daliban makarantu na gwamnatin tarayya bisa zargin yin zagon kasa ga shirin.
An kuma kama wasu masu sayar da abinci guda 10 da ake zargi da hada baki da malamai da kuma ma’aikatan Hukumar don sauya tsarin ciyar da ?aliban firamare wanda gwamnatin tarayya ke kashe makudan kudade akai.
An gano cewa mafi yawan wadanda aka kaman sun fito ne daga makarantar firamare ta Central Primary School da ke Minna, jihar Neja, yayin da aka kuma kama wasu daga makarantun Katcha da ke karamar hukumar Katcha, da kuma Gwada a karamar hukumar Shiroro ta jihar.
Baya ga karkatar da danyen abinci da aka tanada don dalibai a makarantun, an tattaro cewa ana zargin wadanda aka kama da kawar da kiret 30 na kwai da aka shirya don karin kumallon wasu daliban, wadanda ake zargin sun sayar wa masu sayar da abinci na garin.
Sakamakon haka, an tattaro cewa ana sanya yara hudu su raba kwai daya kacal yayin cin abincinsu, yayin da dalibai masu yawa ke tarayya akan kwanon abinci guda.
Jami’ar da ke kula da shirin ciyar da daliban, Misis Amina Guar, lokacin da aka tuntube ta, ta tabbatar da labarin, inda ta ce an sanar da jami’an tsaro game da halin da ake ciki. Ta ce kungiyar ta samu nasarar gano kiretan kwai da wadanda abin ya shafa suka karkatar da su ga masu sayar da shayi a garin Gwada, inda ta kara da cewa:
“Mun sami nasarar kwato kwayayen tare da mayar da su makarantar da abin ya shafa. “Gaskiya ne cewa wasu daga cikin malamanmu a makarantar Firamare ta Central a halin yanzu suna tare da DSS, hasali ma wasunsu sun suma da suka isa wurin.
“Ba mu yarda da cin hanci da rashawa kowane iri ba; ba za mu yarda da ci da gumin yara da basu ji ba basu gani ba,” in ji Guar, tana mai kara da cewa tana sauri don garzayawa ofishin DSS domin sanin halin da ake ciki.
