Amurka Za Ta Taimaki Najeriya Wajen Yaki Da Safarar Miyagun Kwayoyi

Gwamnatin Amurka ta bayyana aniyarta na yin wani shiri domin ?arfafa wa hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun ?wayoyi ta Najeriya NDLEA ta hanyar inganta binciken kimiyya da na sinadarai da kuma inganta hanyoyin tattara bayanan sirri.

A wata sanarwa da jami’in hul?a da jama’a na hukumar Femi Baba Femi ya fitar ranar Litinin ya ce taimakon na Amurka na zuwa ne bayan da shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya bu?aci hakan daga hukumomin na Amurka bayan jerin ganawa da ya yi da manyan jami’an Najeriya da na Amurka.

Baya ga taimako a ?angaren binciken kimiyya da na sinadaran, gwamnatin ta Amurka ta ce shirin zai taimaka wa hukumar wajen samun hanyoyin tattara bayanan sirri ta hanyar na’urori na zamani.

Matakin na zuwa ne bayan da wata ?ungiya mai suna Abdul Samad Rabiu Initiative (ASR Africa) ta bayar da kyautar naira miliyan 500 ga hukumar ta NDLEA domin ?aukar nauyin wasu manyan ayyukan hukumar.

Related posts

Leave a Comment