Da Yiwuwar Mu Mika Abba Kyari Amurka – Ministan Shari’a

Malami ya bayyana hakan ne yayin hira a shirin ‘Politics Today’ na tashar ChannelsTV ranar Litinin. Malami yace: “Akwai lamura da dama da ake tattaunawa kan yiwuwan mikashi ga ?asar Amurka.

“A iya sani na, bangarorin biyu na tattaunawa, suna hada kai kan lamarin bincike, mikashi ga Amurka, da sauran su, Lallai an tabbatar da kamshin gaskiya cikin zargin da ake masa kuma akwai yiwuwan gurfanar da shi da kamashi da laifi idan doka ta kamashi da laifi.”

Hukumar aikin yan sanda (PSC) ta umurci Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya kaddamar da sabon bincike kan alakar dake tsakanin dakataccen jami’i Abba Kyari, da dan damfara, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Wannan umarni ya biyo bayan shawarar da Antoni Janar na kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bada ne.

Related posts

Leave a Comment