Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Kalu, ya ?aryata ra?e-ra?in da wasu ke yi cewa Amirka ta hana ?an takarar shugaban ?asa na APC, Bola Tinubu bizar iznin shiga ?asar ta.
Kalu ya fito a shafin sa na Facebook, ya wallafa cewa, Tinubu ya ?aga tafiyar ce don ?ashin kan sa, amma babu wanda ya hana shi shiga Amurka.
“Tinubu zai bar Najeriya a ranar 4 Ga Disamba, inda zai dira Landan. A can zai gana da jama’a a katafaren ?akin taron Chatham House,” inji Rundunar Kamfen ?in TInubu.
Ta ce a Landan zai yi jawabi a Chatham House, inda zai gabatar da ?udirorin sa, wa?anda za a tattauna su a wurin.
Ita ma cibiyar ta Chatham House ta tabbatar cewa Tinubu zai je ya yi jawabi a ranar 5 ga Disamba, inda zai gabatar da manufofi da ?udirorin sa.
Tun da aka fara zaman muhawara da ‘yan takara, har yau Tinubu bai halarci gayyata ko ?aya a ?asar nan ba. Wasu na mamakin yadda zai ?i halartar muhawarar nan cikin gida, amma kuma zai lula Amurka da wasu ?asashen Turai.
