Rahotanni dake shigo mana yanzu daga masarautar Kwantagora dake Jihar Neja na bayyana cewar Allah yayima mai Martaba Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Sa’idu Namaska rasuwa.
Sarkin ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya da ya yi, ya rasu bayan shafe shekaru 47 bisa karagar mulki.
Muna rokon Allah yagafarta masa dukkanin kurakurensu tareda dukkanin musulmai baki daya alfarmar fiyayyen halitta ANNABI MUHAMMAD S.A.W.
