Al-Mundahana: Gudaji Kazaure Ya Fallasa Sunayen Mutum 7 Da Suka Tsiyata Najeriya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Honorabul Gudaji Kazaure ya bayyana mutane 7 da yace dole sai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kamasu idan yana son mulkinsa ya tafi daidai

Tsohon dan majalisar daga jihar Jigawa, Gudaji Kazaure ya bayyanawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cewa, akwai mutanen da idan bai kamasu ba, kasarnan ba zata zauna daidai ba.

Kazaure ya bayyana hakane a cikin wani bidiyo yayin wata ganawa da shugaban gidan Rediyon Berkete Family Ahmad Isa yayi dashi.

Yace mutanen sune:

Godwin Emefiele

Abdulrashid Bawa

Wadannan mutanen duka suna hannu a yanzu an kamasu.

Sauran sune:

Yace kuma ya kamata a gayyaci tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana ahinda ya bari a ofis wanda Abdulrashid Bawa ya tarar.

Sai kuma tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami

Tunde Buhari

Shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari.

Shugaban FIRS, Muhammad Nnami

Tsohuwar shugabar hukumar Port Authority, Hadiza Bala.

Dr. Bashir Jamo shugaban Nimasa.

Muhammad Bello Koko, shugaban NPA na yanzu

Yace da kuma duka mataimakan gwamnan babban bankin Najariya, Godwin Emefiele ya kamata a kamosu a tambayesu abinda suka sani.

Related posts

Leave a Comment