Hukumar Za?e ta ?asa (INEC) ta bayyana cewa za ta dakatar da shirye-shiryen gudanar da za?u??ukan gwamnoni da za a yi a jihohin Edo da Ondo idan har abubuwan da ‘yan siyasa ke aikatawa ya jawo tarzoma da karya doka.
Kwamishina na ?asa kuma shugaban kwamitin ya?a labarai da wayar da kan masu za?e a hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a Abuja ran Alhamis bayan an yi taro tsakanin hukumar da masu ruwa da tsaki a za?u??ukan inda aka tattauna kan al’amura da dama, ciki har da shirye-shiryen za?u??ukan.
Mista Okoye ya ce hukumar ta yi lura cikin damuwa matu?a da yadda al’amura ke ?ara rinca?ewa wajen abubuwan da jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayan su ke aikatawa tare da furta maganganun tada fitina a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da za?u??ukan.
Ya ce: “Wa?annan abubuwan sun ha?a har da lalata kayan kamfen na abokan adawa kamar su allunan talla tare da ya?ar juna ta hanyar rikici da furta muggan kalamai.
“Ya na da muhimmanci jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayan su su sani cewa akwai dokoki da ?a’idoji da aka shimfi?a wa?anda wajibi ne a bi su a lokacin ya?in neman za?e.
“Hukumar ba za ta yi ?asa a gwiwa ba wajen aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyan ta na tabbatar da an bi doka da oda.
“Saboda haka, lallai ne kada jam’iyyu da ‘yan takara su yi tunanin hukumar ba za ta aiwatar da ?udirin ta na tabbatar da an bi dokoki da ?a’idoji ba kuma ta hukunta duk wani wanda ya za?i ya karya su.
“A shirye hukumar ta ke ta tabbatar da an gudanar da za?e cikin kwanciyar hankali a jihohin biyu da kuma sauran za?u??ukan cike gurbi na Majalisar Tarayya da Majalisun Jihohi.”
Okoye ya ce tilas ne jam’iyyun siyasa su fahimci cewa ana shirin gudanar da za?u??ukan gwamnonin Edo da Ondo ne a daidai lokacin da annobar korona ta mamaye duniya kuma hukumar na aiki tu?uru don tabbatar da cewa an kiyaye dukkan matakan kare kai daga cutar kamar yadda hukumar za?en da hukumomin kiwon lafiya su ka tanadar.
Ya ce a yayin da annobar ta ke ragargazar jama’a, ya zama wajibi kada a ?ara jibga wa mutanen jihohin Edo da Ondo nauyin fitinar tashin hankali a lokacin za?u??ukan.
“Tilas ne jam’iyyu su tuna da cewa akwai lokutan da dokokin tsarin mulki da na hukumar za?e su ka shata wa za?u??ukan Edo da Ondo kuma barazana ko ainihin aiwatar da tarzoma zai iya rusa wa?annan lokutan har su haifar da rikici da ya danganci tsarin mulki.
“Hukumar za ta ci gaba da tuntu?ar masu ruwa da tsaki a jihohin biyu a kan bu?atar da ke akwai ta gudanar da za?e cikin kwanciyar lumana, musamman ganin cewa ta kashe ma?udan ku?in jama’a don shirya za?u??ukan.
“Hukumar za ta ?auki babban mataki kan duk wani abu da ‘yan siyasa za su yi wanda zai tada hankalin jama’a.”
Okoye ya ce za ta yi aiki tare da ha?a gwiwa da hukumomin tsaro don magance duk wani abu ko wata barazanar tada hankali kafin da kuma lokacin za?u??ukan.
“Tilas ne hukumomin da aka ?ora wa alhaki a za?u??ukan, musamman wa?anda su ka danganci mahance rashin zaman lafiya da ya?a maganganun ?atanci da yin amfani da kafofin ya?a labarai ta hanyar da ba ta kamata ba, su tashi tsaye a aikin su don tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka kama ya na karya doka.”
Hukumar ta kwantar wa da al’ummomin Edo da Ondo hankali da cewa ta ?udiri aniyar yin za?e bisa adalci da lumana a jihohin biyu, sannan ta yi kira a gare su da su mara wa shirin goyon baya.
