Agaji : Za A Fara Jefowa ‘Yan Gudun Hijira Abinci Daga Jirgin Sama – Sadiya

Gwamnatin tarayya ta fara shirye-shiryen bayar da agaji ga ?auyukan arewa maso gabas ta hanyar amfani da jiragen sama domin cilla wa ‘yan gudun hijira abinci.

Ministar kula da ayyukan jin-?ai da kare afkuwar bala’i Sadiya Farouk, a ranar Lahadi ta shaida wa ‘yan jaridu a Maiduguri cewa za a fara amfani da jiragen sojojin sama a Nijeriya domin cilla abinci da sauran kayayyakin tallafi kamar bargo da dai sauransu ga ‘yan gudun hijirar da ba sa gidajensu.

Ta bayyana cewa akwai matsaloli da ma’aikatan bayar da agaji ke fuskanta na kai wa ga jama’ar da ke cikin ?auyen kaya, inda ta ce cilla abincin ne mafita ga ?auyukan da mota ba ta iya zuwa.

Related posts

Leave a Comment