Adamawa: ‘Yan Takarar APC Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi

Rahotannin dake shigo mana daga Yola babban birnin jihar Adamawa na bayyana cewar ‘Yan takarar shuagabanin kananan hukumomi da Kansilolinsu na Jam’iyar APC sun yi Allah wadai da sakamakon za?en kananan hukumomi da aka gudanar kwananan a jihar.

Honorabul Ahmed Rufa’i ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatarwa manema labarai jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Yola.

Ahmed Rufa’i yace lamarin baiyi dadi ba ko kadan kasancewar sun shiga sa?o-sa?o domin neman kuri’a amma ace wai basu da kuri’ar da zai basu damar cin zabe.

Don haka ne suke jan hankali hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar da su kasance masu yin adalci a lokacin da ake gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar.

Honorabul Idris Sani ?an takarar Shugaban karamar hukumar Yola ta arewa shima ya nuna rashin jin dadinsa dangane da yadda aka bayyana sakamakon zaben, asali ma ba a tura kayayyakin zaben a rumfunan zabe a kan lokaci ba don haka ba a musu gaskiyaba.

Shima ?an takarar Shugaban Karamar hukumar Gombi Abubakar Saleh ya bayyana cewa rashin gamsuwarsa da wannan sakamokon zabe da hukumar zaben jihar ta fitar dan haka akwai bukatar sake duba sakamakon zaben.

Related posts

Leave a Comment