Adamawa: Shugaban Dillalan Mai Ya Yi Kiran Hadin Kai Don Fuskantar Zaben 2023

A yayin da aka fuskanci fara gangamin neman zabe domin gudanar da babban zaben shekara ta 2023 an kirayi ‘yan Najeriya da su kasance masu hada kansu a koda yaushe da kuma nesanta kansu da yin siyasar ?angaranci ko addini domin samun haydin kan kasa da wanzar da zaman lafiya a fa?in Najeriya baki daya.

Shugaban kungiyar Dillalan Man fetur na kasa IPMAN shiyar Jihohin Adamawa da Taraba Alhaji Dahiru Buba ne ya bayyana haka a zantawarsa da Wakilinmu a Yola.

Alhaji Dahiru Buba yace hadin kai a tsakanin al’umma abune da yake da matu?ar muhimmanci don haka akwai bukatan ‘yan Najeriya suyi karatun ta natsu domin samarwa kansu hanyoyin da za su taimaka wajen cigaban kasa da kuma samar da zaman lafiya.

Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su kara maida hankali wajen yin addu’o’i a koda yaushe wanda a cewarsa haka zai taimaka wajen kawo karshen kalubalen tsaro dake ciwa gwamnatin kasar nan tuwo a kwarya.

Alhaji Dahiru ya kuma kirayi matasa da su sanifa sune ?ashin bayan al’umma don haka suma suna da gudunmawa da zasu iya bayarwa wajen wanzar da zaman lafiya dama cigaban kasa baki daya. Tare da shawartarsu da kada su bari ‘yan siyasa suyi amfani da su wajen yin bangar siyasa ko abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin al’umma.

Related posts

Leave a Comment