Wata babbar kotu a Yola babban birnin Jihar Adamawa karkashin jagorancin Mai sharia Mohammed Danladi a ranar Talata ta kori Sanata Ishaku Abbo a matsayin dan takarar Sanatan Adamawa ta Arewa a karkashin jamiyyar APC a zaben bana.
Kotu ta kori Sanata Abbo ne bisa hujjar cewa mazabarsa da ke karamar hukumar Mubi ta Arewa ta kore shi daga jamiyyar.
Mai sharia Danladi, ya bayyana cewa Sanata na da nasaba da kudurin da majalisar zartarwar jamiyyar APC reshen karamar hukumar Mubi ta Arewa ta yanke na korar shi daga jamiyyar a ranar 7 ga watan Oktoba 2022.
Kotun ta kuma yi watsi da cewa Sanata Abbo ba shi da hurumin samun wani hakki ko wata gata da aka bai wa yan jamiyyar APC.
Ku tuna cewa a ranar 7 ga watan Oktoban 2022 ne shugaban karamar hukumar Mubi ta Arewa ya amince da korar Sanatan kamar yadda kwamitin ladabtarwa na jamiyyar ya bayar.
Kotun ta kuma hana jamiyyar APC da Sanatan ke neman tazarce a karkashinta kar ta amince da shi a matsayin dan takararta, inda ta ce ba zai iya zama dan takarar jamiyyar ba a zabe mai zuwa.

