Rahotanni daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar An kirayi ma’aikatan kananan hukumomi da su kasance masu hada kansu a koda yaushe domin ganin an samu cigaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin wato NULGE a jiha dama kasa baki daya.
Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi a Najeriya shiyar jihar Adamawa Hamman Jumba Gatugal ne yayi wannan kira a lokacin da yake karban rantsuwa a matsayin shugaban kungiyar a jihar Adamawa,
An dai gudanar da bikin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar a gidan saukan baki na kungiyar dake Yola.
Hamman Jumba yace hadin kai a tsakanin ?a?an kungiyar zai taimaka wajen samun cigaban kungiyar harma da samar da zaman lafiya mai dorewa a cikin kungiyar yadda ya kamata.
Ya kuma kirayi ‘yan Najeriya da su maida hankali wajen yin addu’a koda yaushe domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin matsalar tsaro a fadin Najeriya baki daya.
Harwayau Hamman Jumba Gatugal ya tabbatarwa membobin kungiyar cewa zaiyi iya kokarinsa domin ganin cewa ma’aikatan kananan hukumomi sun samu hakkinsu da kuma cigaban kungiyar tasu.
Shima anshi jawabi Shugaban kungiyar malamai ta kasa NUT Shiyar jihar Adamawa Rodney S Nathan ya bayyana yanayin da malaman makarantu firamare ke ciki na rashin biyansu Albashin mafi karanci wanda a cewarsa hakan ya sanyasu ciki wani yanayi na matsalar rayuwa.
Don haka nema ya kirayi gwamnati da ta duba matsalar domin magancesu wanda hakan zaisa malamain su samu walwala yadda ya kamata.
