Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sama da ‘yan Majalisar Dattawa 73 sun bayyana aniyar amfani da karfin iko wajen tabbatar da sabuwar dokar zaben da shugaba Muhammadu Buhari ya ki sanyawa hannu.
An ruwaito Sanata George Sekibo daga jihar Rivers na cewa tuni ‘yan majalisar daga jam’iyyu daban-daban suka fara sanya hannu kan takardar amincewar.
Sanatan wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP ne, ya kara jaddada aniyarsu a tattaunawa da gidan talbijin na Channels, a ranar Talata.
“Don me ya sa shugaban kasa zai ki amincewa da zaben fidda gwani na ‘yar tinke? Najeriya ba kamfaninsa ba ce, wannan kasa ce da cikakken iko da kuma ta ke da ‘yan majalisu. Kuma za mu tabbatar da wannan doka.
“Sashe na 58 na kundin tsarin mulki ya ba mu damar daukar matakin. Dan haka idan tsarin mulki ya ba mu dama, za mu yi amfani da hakan. Kuma tuni mu ka samu ‘yan majalisa 73 daga jam’iyyu daban-daban da suka rattaba hannun amincewa da matakin tabbatar da dokar nan, za kuma mu yi hakan.”
