Adamawa: An Gudanar Da Zaben Shugabannin APC

An gudanar da zaben shugabanin jam iyar A P C a matakin kananan hukumomi a jahar Adamawa.

Muryar yanci ta ziyarci sakatariyar Jam iyar A P C dake jahar Adamawa inda aka gudanar da zaben shuwagabanin jam iyar na karamar hukumar yola ta Arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.

A zantawarsa da manema labarai Alhaji Abdullahi Wali ya baiyana farin cikinsa dangane da yadda aka gudanar da zaben ba tare da wata matsalaba.

Don haka nema ya kirayi yan jam iyar da su kasance masu hada kansu a koda yaushe domin samun cigaban jam iyar a jahar dama kasa baki daya.

Alhaji Abdullahi Wali ya kuma kirayi wadanda basuyi nasaraba da suzo a hada kai domin ciyar da jam iyar gaba.

Shima anaahi jawabi Alhaji Abubakar Baba Zango ya baiyana gamsuwarsa dangane da yadda aka gudanar da zaben wanda akayishi cikin tsanaki ba tare da tashin hankaliba.

Shima shawartan yan jam iyar yayi da su hada kai domin yin aiki kafada da kafada wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen daga martaban jam iyar ta A P C baki daya.

Ibrahim Rabi u wanda kuma shinema yayi nasaran lashe shugaban jam iyar A P C a karamar hukumar yola ta Arewa ya baiyana jin dadinsa dangane da wannan nasara da yayi.

Ya kuma tabbatar da cewa zai aiki tare da dukkanin yan jam iyar kafada da kafada domin ganin jam iyar ta samu nasara a zaben shekara ta dubu biyu da aahirin da uku.

Ya kuma shawarcin yan Najeeiya da sucigaba da yin adu o i domin samar da zaman lafiya jaha dama kasa baki daya.

Related posts

Leave a Comment