Farfado Da Tattalin Arziki: Buhari Zai Sayar Da Kamfanonin Gwamnatin Tarayya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ?arkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin sayar da ko mika wasu kadarorin kasuwanci mallakin kasa ga masu saka hannun jari masu zaman kansu.

Wannan mataki na daga cikin matakin da gwamnatin Nijeriya ta dauka na farfado da kamfanoni a shekarar 2021 da kuma bayanta.

Ofishin Kamfanoni Mallakin Gwamnatin Tarayya (BPE) ya gayyaci masu son saka hannun jari don cin gajiyar tallafin da gwamnati ta gabatar da siyan cikin wadannan kamfanoni da aka ayyana.

Mun tattaro muku jerin kamfanonin da gwamnati ta amince da yin wannan harkalla dasu, kamar haka:

1- The Nigeria Integrated Power Projects (NIPPS) da ke a Calabar. 2-Geregu, Omotosho da Benin (IHOVBOR). 3- Transmission Company of Nigeria (TCN) Zungeru. 4-Hydro Plant Nigerian. 5-Postal Service (NIPOST) Abuja. 6- Environmental Protection Board (AEPB) . 7-The Nigeria Film Corporation (NFC) Federal Capital Territory. 8-Water Board Abuja International Conference Centre (AICC). 9-Save Sugar Company Lagos. 10-International Trade Fair Complex (LTFC). 11-Tafawa Balewa Square (TBS). 12-River Basins Developments Authorities (RBDAS). 13- Bank of Agriculture (BOA) 14 -The Nigeria Commodity Exchange (NCX)

Related posts

Leave a Comment