Adamawa: An Damke Uban Da Ya Kashe ‘Yarsa

Rundunan yan sandan jahar Adamawa yanzu haka tana tana tsare da wani magidanci mai suna Muhammed Saleh mazaunin karamar hukumar Mayo Belwa dake jahar Adamawa bisa zarginsa da hallaka yarsa mai suna Aisah yar shekara goma sha shida da haifuwa.

A zantawarsa da muryan yanci magidancin da ake zargi da kaahe yarsa wato Muhammed Saleh a shelkwatan rundunan yan sandan dake yola yace shi da taimakon abokansa ne suka kashe yarinyar ta hanyar yi mata duka wanda kuma hakan yayi sanadiyar tafiyarta lahira.

Ya kuma baiyana cewa bayan sun kashetan ne suka barta a dajin wanda hakan yasa aka gudanar da bincike sannan aka gano gawar yarinyar.

Shidai Saleh yace ya aikata hakane bisa zargin cewa ba yarsabace biyo bayan yadda Uwar yarinyar tace masa daman tazo gidansa da cikin yarinyar acewarsa.

A yayinda muryar yanci ta tuntubi yadikon yarinyar mai suna Aisha tace baban nata ya fita da yarsa ne da sunan zai saya kifi ta kawo gida dagan bata gantaba dashi sai bayan kwana daya, inda yazo yana tabbayarta ina Aisha sai tace masa ai tunda kuka fita jiya har yanzu bata dawoba.

Inda shima ya shiga nemanta daga bisani dai a shigar da maganan afishin yan sanda dake Mayo Belwa inda aka gudanar da bincike aka gano cewa shine da kansa ya kashe yar nasa.

Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatarwa muryar yanci aukuwar lamarin yace sun samu rahoton faruwar lamarin wanda hakan yasa kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Muhammed Ahmed Barde ya bada umurnin gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

A yanzu haka dai magidancin yan sashin binciken manyan laifuka a shelkwatar rundunan yan sandan domin cigaba da bincike kuma da zaran an kammala bincike za a gurfanar dashi a gaban kotu domin ya fuskaci shari a.

D S P Suleiman Yahaya Nguroje ya kirayi al ummar jahar ta Adamawa da su kasance masu baiwa hukumomin tsaro hadin kai da goyon baya da kuma basu wasu bayanai wanda acewarsa hakan zai basu damar dakile irin wadannan laifuka a tsakanin al umma baki daya.

Related posts

Leave a Comment