Shahararren mawa?in siyasar nan a Najeriya, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, zai saki sabuwar wa?arsa wacce ya ranga?awa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, domin goge laifin da yan ?asar ke ganin ya yi musu.
Masoya Buharin dai na ci gaba da tambayar ina aka kwana a kan batun ku?in da suka tura domin yi wa masoyinsu wa?a.
Wa?ar dai za ta zo da sabon salo domin ba irin wacce mawa?in ya saba yi ce a shekarun baya ba, kamar yadda mawa?in ya fa?a, ana sa ran sakin sabuwar wa?ar nan ba da jimawa ba, kamar yadda wata majiya daga mawa?in ta bayyanawa sashin hausa na APA.
Idan ba ku manta ba a ?arshen watan oktoba, a shekarar da ta gabata, mawa?in ya bayyana cewa “ba zai sake yiwa shugaban ?asa Muhammadu Buhari wa?a ba, sai idan masoyan shugaban sun biya shi ku?in wa?ar, inda ya nemi masoya Buharin da su tura masa naira 1,000 ?ai-?ai kafin ya yi wa shugaban wa?ar”.
