Shirin raya kasashe na Majalisar ?inkin Duniya (MDD) wato UNDP ya ce adadin ?ananan yara da za su mutu zai iya kaiwa miliyan ?aya nan da shekara ta 2030 idan ba a magance matsalar ba.
UNDP ta ce yara 170 ne suka yi ta mutuwa a kowace rana a Najeriya a shekarar 2020 da ta wuce sakamakon rikicin Boko Haram da ake fama da shi a arewa maso gabashin kasar.
A cewar rahoton, yawan kananan yaran da ke mutuwa a yankin zai iya kaiwa 240 a kowace rana nan da zuwa shekara ta 2030.
Lamarin kamar yadda shirin na raya ?asashe na MDD ya bayyana, ya fi shafar yara masu rauni `yan kasa da shekara biyar, wa?anda ke fama da yunwa da kuma cutuka sakamakon karancin ruwan sha mai inganci.
Yanayin rikici, musamman yadda ya ki ci ya ki cinyewa, sannan kuma ake mirginawa da shi daga wata shekara zuwa wata, yana mummunan tasiri a kan kananan al’umma musamman yara.
