Lokaci Ya Yi Da Za A Fara Tura Masu Yi Wa Kasa Hidima Filin Daga – Shugaban NYSC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar NYSC ta masu yan yi wa kasa hidima, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya ce masu yi wa kasa hidimar suna cikin jami’an tsaron Nijeriya kuma ana iya basu horon zuwa yaki idan bukatar hakan ta taso.

Janar Ibrahim ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da aka yi da shi a ranar Laraba yayin da ya ke magana kan batun kiraye-kirayen da wasu ke yi na cewa a soke tsarin yi wa kasa hidimar.

Ya bayyana cewa irin horaswar da aka bawa masu yi wa kasa hidimar na makwanni uku na shirya su tamkar sojoji. “Masu yi wa kasa hidima suna zaman ko ta kwana ne, Suna cikin jami’an tsaro a tsarin kasar nan.

Don haka, idan akwai yaki mai tsanani, yan NYSC dinmu masu ilimi ne, sun karantu don haka za a iya horas da su. Za ka ga irin horaswar da ake basu da sauransu.

“Ka duba yadda ake basu horaswa cikin makwanni uku kacal a sansanin masu yi wa kasa hidima. Kamar sojoji suke. Za ka ga mai yi wa kasa hidima mace na busa algaitar sojoji, tana buga ganga.”

Janar Ibrahim ya ce a yanzu ne NYSC ke da muhimmanci sosai duba da cewa akwai wasu da ke son ballewa daga kasar.

Ana wajabta yi wa kasa hidimar ne ga dukkan wanda ya kammala digiri ko HND kuma bai haura shekaru 30 da haihuwa ba a Nijeriya muddin ba shi da wata matsala ta musamman.

Related posts

Leave a Comment