Tsohon shugaban rundunar soji, Tukur Buratai, yace magajin sa, Ibrahim Attahiru, ya kama hanyar sanya Najeriya alfahari da ?ora ?asar kan turba bayan lalubo bakin zaren warware matsalolin Najeriya da ya yi, sai dai kuma mutuwa ta yi mishi gaggawa inda ta ?auke shi a daidai lokacin da Najeriya ke bu?atarsa.
Janar Buratai yace a fili yake marigayin ya ?auko hanyar kawo ?arshen ayyukan ta’addanci a ?asar nan kafin wannan mummunan lamarin yayi sanadiyyar mutuwarsa, wanda dukkanin jama’a sun shaida hakan.
Ya bayyana hatsarin da abin tausayi ga yan Najeriya, yace Janar Attahiru da jami’an da suka rasu tare da shi sun bar tarihin da ba za’a ta?a mantawa dashi ba, a tarihin Najeriya har abada.
A cewarsa, hatsarin yayi matu?ar girgiza shi kamar yadda ya girgiza yan Najeriya saboda Attahiru ya mutu amma yabar mutane da ya?inin irin nasarorin da ya samu a ?angaren ayyukan soji.
Buratai yace:
“Attahiru ya kama hanyar sanya ?asar mu alfahari bisa najimin ?o?arin da yake yi wajen magance matsalar tsaron da muke fama da ita, bani da tantama a kan ?wazon shi saboda yayi aiki a ?ar?ashina a ?angare daban-daban.”
“Nayi matu?ar ka?uwa da ba?in cikin mutuwar Janar Ibrahim Attahiru, a hatsarin jirgin sama, wanda ya ri?e mu?amai da dama kafin zaman shi shugaban rundunar soji.”
“A madadin iyalaina ina mi?a sa?on ta’aziyya ga shugaban ?asa Buhari, iyalan shi, ministan tsaro, jami’an sojin ?asa da na sama bisa mutuwar wa?annan manyan jami’ai yayin da suke cikin aiki.”
Buratai ya ro?i hukumomin tsaro su tabbatar da ayyukan da wa?annan mutanen suka ?auko bai tafi a banza ba, ta hanyar cika musu burinsu a ayyukan da suka fara.
