Mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci Musulmi su rubanya addu’o’i a kwanaki 10 na karshen watan Ramadan domin samun tsaro da aminci a Najeriya.
Sarkin Musulmin kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ya bukaci ’yan Najeriya da su zama masu lura a yankunansu game da matsalar tsaro da ke addabar kasar.
Ya yi kiran a yawaita yin HasbunaLlahu wani’mal wakeel; Astagfirullah; La hawla walakuwata ilabiLlahi-l-Aliyi-l-Azeem; La ilaha illa anta Subuhanaka inikuntu mina zalimeen, Allah Ya kawo wa kasar sauki.
“Majalisar na kuma kira ga Musulmi su mara wa duk yunkurin tabbatar da dorewar Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya, kamar yadda yake kunshe cikin takardar sanarwa Mataimakin Babban Sakataren Majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya sanya wa hannu.
Sarkin Musulmin ya kuma jaddada muhimmancin ’yan kasa su rika taimaka wa hukumomin tsaro domin magance matsalar da ta zama ruwan dare.
Ya yi kiran ne yayin nuna damuwa game da yadda rashin tsaro ya haifar da kashe-kashe da kuma tsoro, zullumi, rudani, da a zukatan ’yan Najeriya.
