Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Harbe ?an Jarida Da Yin Gaba Da Mutane Da Dama

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar ‘yan bindiga ?auke da muggan makamai sun kashe wani ?an Jarida mai aikin daukar hoto a sashen labarai na karamar hukumar Jibia, Ibrahim Dankabo, ranar Litinin da yin gaba da mutane da dama a wani farmaki da suka kai.

Hakazalika Yan ta’addan kuma sun yi garkuwa da matafiya da yawa a yankin, inda suka kutsa cikin daji da su a cewar wata majiya daga yankin.

Wani shugaban yankin, Gide Suleiman, ya shaidawa manema labarai cewa an harbe Dankabo a Kukar-Babangida a karamar hukumar Jibia inda yake rayuwa, lokacin da ya ji ihun wata makwabciyar sa lokacin da ake yunkurin garkuwa da mutane, ya fito domin ganewa idanunsa.

Yan bindigar sun yi awon gaba da matar, wadda mahaifiyar wani mai sarautar gargajiya ce a Kasar Nijar a cewar majiyar.

Kuma, wasu mazauna yankin sun ce maharan sun yi garkuwa da matafiya da dama akan titin Katsina-Jibia wanda da yawan su yan garin Magamar Jibia ne.

Mai magana da yawun yan sandan Katsina ya ce bai samu labarin harin na Jibia ba.

Related posts

Leave a Comment