Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya rage hasashen da ya yi a kan bun?asar tattalin arzikin Najeriya na 2024 zuwa kashi 3.1.
Wannan na ?unshe ne a cikin sabon rahoton asusun a kan tattalin arzikin duniya na watan Yulin 2024, wanda aka wallafa a ranar Talata.
IMF ya ce an samu wannan koma baya ne saboda rashin bun?asar tattalin arzikin a zangon farko na wannan shekarar.
A bisa sabon hasashen, an samu raguwar kashi 0.2 a bun?asar tattali arzikin Najeriya, wanda a baya aka yi hasashen zai tashi da kashi 3.3 cikin ?ari.
Amma IMF ta ce tattalin arzikin Najeriyar zaii bun?asa da kashi 3.0 a cikin 2025.
Dama dai hukumar ?ididdiga ta Najeriya ta fitar da wasu al?alumma da ke nuna cewa tattalin arzikin ?asar da ake samarwa a cikin gida zai ragu zuwa kashi 2.98, a zangon farko na 2024, daga kashi 3.46 da aka samu a zangon ?arshe na 2023.
