‘Yancin Kan Kananan Hukumomi: Tinubu Ya Yaba Hukuncin Kotun Koli

Shugaban ya bayyana cewa, babban abin da ke kawo cikas ga ci gaban kasar nan shi ne rashin gudanar da ayyukan kananan hukumomi masu inganci, saboda akwai rashin gudanar da mulki a matakin farko na tsarin zamantakewa da siyasa.

Shugaban ya jaddada cewa a yanzu alhakin shugabannin kananan hukumomi ne su tabbatar da cewa duk ‘yan Najeriya mazauna wannan matakin sun gamsu da samun ayyukan da suka dace da bukatun su.

Ya ce, “Ajandar sabunta fata ta shafi al’ummar kasar nan, a kowane mataki, ba tare da la’akari da addini, kabila, jinsi, siyasa, ko wani layi na wucin gadi da suka ce akwai a tsakaninmu ba, kasar nan ta mu ce baki daya. Bisa ga wannan hukunci, al’ummarmu – musamman talakawa – za su iya yi wa shugabanninsu hisabi a kan abin da aka aika a asusun kananan hukumomi, kuma a yanzu dole ne a samar da ayyuka ba tare da uzuri ba.

Wannan hukunci ya tabbata a fili. cewa za mu iya amfani da hanyoyin da suka dace wajen gyara kasarmu da sake fasalin tattalin arzikinmu don ganin Najeriya ta zama wurin zama mai kyau da kuma kyautata zamantakewa ga daukacin al’ummarmu.”

Related posts

Leave a Comment