Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin ?ungiyoyin ?wadago a fadarsa a Abuja.
Shugaban ya ce yana bu?atar lokaci kafin ya aika da ?udirin neman ?arin albashi mafi ?an?anta zuwa Majalisar Tarayya.
Sai dai bayan ganawar, shugaban ?ungiyar ?wadago ta NLC Joe Ajaero, ya ce suna nan kan bakarsu ta neman N250,000 a matsayin albashi mafi ?an?anta ga ma’aikatan Najeriya.
Ya ce tattaunawa suka yi da shugaban amma ba sasanci ba kan batun ?arin albashin.
“Mun amince mu koma mu yi nazari kafin makon gobe,” inji Kwamred Ajaero.
Da aka tambaye shi game da matsayarsu kan N250,000 sai ya ce “ba mun tafi ba ne mu yi ciniki amma muna nan kan bakarmu har sai mun kammala tattaunawa.
Sai dai karamar ministan ?wadago Nkeiruka Onyejeocha ta ce an yi tattaunawa mai ma’ana tsakanin shugaban ?asa da kuma shugabannin na ?wadago.
Ta bayyana fatan za a daidaita nan ba da jimawa ba.
