Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu, ya yi bayanin cewa matsalar talauci ba ?an Najeriya ka?ai ta shafa ba Shugaba Tinubu ya bayyana cewa akwai talauci da wahala a ?asar nan amma hakan matsala ce wacce ta shafi dukkanin duniya ba Najeriya ka?ai ba Ya yi nuno da cewa dole ne a magance matsalar ayyukan ?an bindiga da ta’addanci domin manoma su samu damar noma abinci a gonakinsu
Shugaban ?asa Bola Tinubu ya bayyana cewa ba ?an Najeriya ne ka?ai ke fuskantar talauci a duniya ba. Shugaban ?asan wanda ya amince cewa akwai talauci da wahala a ?asar nan, ya ce dole ne a magance ?alubalen.
Ya yi bayanin cewa ?aga cikin hanyoyin magance ?alubalen ita ce kawar da ?an bindiga da ?an ta’adda ta yadda manoma za su iya komawa gona.
Tinubu ya gana da ?an majalisa
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata, Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya kar?i ba?uncin tawagar ?an majalisar tarayya, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Tawagar ta samu jagorancin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, mataimakinsa, Barau Jibrin da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu da sauransu, rahoton The Punch ya tabbatar.
“Eh akwai talauci, ana shan wuya a ?asar nan. Ba mu ka?ai ba ne ke fuskantar hakan, amma dole ne mu fuskanci ?alubalenmu.” “Dole ne mu samo hanyar da za mu kawar da ayyukan ?an bindiga da ta’addanci ta yadda manoma za su iya noma abinci a gonakinsu.”
Idan babu hanyoyi masu kyau da za a kawo abincin ga jama’a, ko da an noma abincin amma ana yin asarar kaso 60-70%, za a samu babbar matsala.”
