Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yi magana kan dalilan da yasa jihar ta kasa magance matsalar hare-haren ?an bindiga. Gwamnan ya yi nuni da cewa an kasa shawo kan matsalar ne saboda ?an sa-kai ba su da ingantattun makamai.
“?an sa-kai ba za su iya ri?e abin da ya wuce ?an ?ananan bindigu ba, amma wa?annan ?an bindigan suna zuwa ne ?auke da AK-47 da mugayen makamai. Wannan shi ne halin da muka tsinci kan mu a ciki.”
Gwamnan ya sake yin kira kan muhimmancin samar da ?an sandan jihohi domin kawo ?arshen matsalar rashin tsaro, Uba ya yi nuni da cewa samar da ?an sandan jihohin zai ba mutanen ?auyuka, damar ri?e makaman da za su kare kansu da su.
“Wannnan shi ne dalilin da ya sa wasu daga cikinmu suka dage cewa muna bukatar a samar da ?an sandan jihohi. “Idan aka samar da ?an sandan jihohi, za a ba su dama bisa dokar kundin tsarin mulki su ri?e makamai ciki har da AK-47.
