‘Yan Majalisar wakilai sun gayyaci ministan lafiya Ali Pate bisa Zargin karkatar da dala Miliyan 300 na kudaden yaki da cutar zazzabin cizon sauro ba bisa ka’ida ba.
Kwamitin Majalisar wakilai mai yaki da cutar zazzabin cizon sauro, HIV/AIDS, da tarin fuka, Ya gayyaci Mohammed Pate, ministan lafiya da walwalar jama’a, kan zargin karkatar da dala miliyan 300 na ku?a?en yaki da zazzabin cizon sauro.
Shugaban kwamitin,Amobi Ogah ne ya sanar da hakan a wani zama da suka yi a Abuja A Yau Talata.
Ogah ya nuna rashin jin dadinsa da rashin halartar babban sakatariyar ma’aikatar a taron kwamitin, inda yace idan har ta gaza bayyana bayan sammaci uku, za a kama ta.
“Maleriya ta zama annoba a Najeriya, duk da cewa Gwamnati ta ware kudade tun daga Shekarar 2021. Sai dai a mafi yawan lokuta ma’aikatan Gwamnati na haifar da kalubale,” inji Amobi Ogah.
Ya jaddada cewa wannan ita ce gayyata ta uku da aka yi wa sakatare na dindindin domin fayyace yadda ake amfani da kudaden. Kwamitin na neman amsoshi kan ko an yi amfani da ku?a?en da kuma inda suke a halin yanzu.
“Shin sun yi amfani da kudin? Idan ba su yi amfani da ku?in ba, ina ku?in? Magana ce mai sau?i. Amma sun yi ta gudu suna kiran mutane iri-iri domin su yi magana da mu,” inji shi.
