Bauchi: An Tsinci Gawar Hakimin Riruwai Da ‘Yan Bindiga Suka Sace

IMG 20240319 WA0082

‘Yan bindiga ne sun kashe hakimin kauyen Riruwai da ke gundumar Lame a karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.

PREMIUM TIMES ta samu labari a ranar Litinin cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka sace Garba Badamasi daga kauyen a ranar Juma’a kuma ba a san inda yake ba har zuwa ranar Lahadin da ta gabata inda jami’an tsaro suka gano gawar sa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kai gawar zuwa fadarsa da ke Lame inda aka yi masa sallar jana’iza kuma aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Muna cikin fargaba matuka, domin babu wanda ya san abin da zai biyo baya, da kuma wanda za su sake kamawa su kashe.

“ Ta’addanci ya karu matuka a karamar hukumar Toro, musamman a dajin Magama Gumau, gurguzu, da dajin Bura da ke karamar hukumar Ningi, wadannan yankuna ne suka fi fama da matsalar ta’addanci a jihar.

“A daren Juma’a, lokacin da ‘yan bindigar suka zo kauyenmu, sai suka fara harbe-harbe ta ko’ina kafin nan suka yi awon gaba da hakimin,”

Related posts

Leave a Comment