Yan bindiga ne sun kashe hakimin kauyen Riruwai da ke gundumar Lame a karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.
PREMIUM TIMES ta samu labari a ranar Litinin cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka sace Garba Badamasi daga kauyen a ranar Jumaa kuma ba a san inda yake ba har zuwa ranar Lahadin da ta gabata inda jamian tsaro suka gano gawar sa.
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kai gawar zuwa fadarsa da ke Lame inda aka yi masa sallar janaiza kuma aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Muna cikin fargaba matuka, domin babu wanda ya san abin da zai biyo baya, da kuma wanda za su sake kamawa su kashe.
Taaddanci ya karu matuka a karamar hukumar Toro, musamman a dajin Magama Gumau, gurguzu, da dajin Bura da ke karamar hukumar Ningi, wadannan yankuna ne suka fi fama da matsalar taaddanci a jihar.
A daren Jumaa, lokacin da yan bindigar suka zo kauyenmu, sai suka fara harbe-harbe ta koina kafin nan suka yi awon gaba da hakimin,

